Hukumar Tsaro ta Sibil difens a Jahar Benue ta kama wata da ake zargin tana safarar mutane, da ƴan mata 6, wanda ta shirya yin safarar su zuwa ƙasar waje.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar waɗanda ake zargin mai suna Mnena Kwaghmande an kama ta a yankin Gboko ta Jahar Benue a ranar 5 ga watan Janairun Shekarar 2022, da waɗanda zata yi safarar su zuwa Ƙasar Burkina-Faso.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Gurfanar Da Wanda Ake Zargi Da Tashin Gobara A Majalisar Dokokin Afirka Ta Kudu Da Ta’addanci
Kwamandan Hukumar Dr Philip Okoh a lokacin da yake gabatar da waɗanda ake zargin, yace wadda ake zargin ta bayyana cewa ta gayawa iyayen yaran cewa zasu taimaka mata ne a wurin saida Abincin ta na Burkina-Faso.
Ƴan matan dai an ɗauko su ne daga Ƙaramar Hukumar Vandeikya ta Jahar Benue.
Kwamandan yace “muna nuna wa al’umma abinda muke yi domin bada tsaro a Jihar Benue domin tabbatar da zaman lafiya.
Ya gargaɗi iyaye dasu guji bada ƴaƴan su ga mutanen da suka yi masu alƙawarin samun kuɗaɗe a ƙasashen waje, yana mai nuni dacewar da yawan su sun shiga matsala a can.
Kwamandan ya kuma gabatar da wani mai satar Na’urar POS da ake kira da suna Iorchivir Caleb, Wanda aka kama shi da bindiga ƙirar fistin, a lokacin da yake ƙoƙarin yiwa wani sata akan hanyar George Akume a Makurɗi Babban birnin jahar a ranar 7 ga watan Janairun wannan shekarar.
Comments 1