By Abbas Yakubu Yaura
Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta amince da hukuncin kisa ga Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar Noble Kids Academy da ke Kawaji a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano.
Tanko, mai makarantar, ya amsa laifin kashe yarinyar da bata da laifi da maganin bera.
Ya yanyankata ya binne ta a asirce a daya daga cikin rassan makarantar.
An dai yi garkuwa da yarinyar ne a watan Disamba kuma aka kashe ta ba da dadewa ba, duk da cewa wadanda suka sace ta sun bukaci a biya su Naira miliyan 6.
A yayin da ake kokarin karbar wani bangare na kudin fansa ne jami’an tsaro suka kama mamallakin makarantar.
An dai yi ta cece-ku-ce kan kisan, inda aka yi ta yada #neman ayiwa Hanifa adalci a shafukan sada zumunta a ‘yan kwanakinnan.
A cikin wani faifan bidiyo, wanda yanzu haka ya fara yaduwa, Malam Abdallah Gadon Kaya, wani Malami a Kano, ya nemi a kashe Tanko kamar yadda ya kashe Hanifa.
Ya ce kamata ya yi a kashe mai gidan a bainar jama’a, inda ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Ganduje za su iya yin hakan.
“Rayuwar shi (Tanko) bai wuce rayuwar yarinyar nan ba, yadda ya kashe ta, shi ma a dauki ransa a bar shi a bainar jama’a don kada wani ya sake aika ta irin hakan.”
Uwargidan shugaban kasar ta sake wallafa bidiyon a shafinta na Instagram, inda ta bayyana goyon bayanta ga kiran da malamin ya yi.
Ta rubuta “Muna bayan matsayin Mallam.”