Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa ta zuba ido sosai kan asusun ajiyar banki na ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa masu neman mukamai daban-daban a zaben shugaban kasa na 2023.
A cewar shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, kowane dan takara za a wajabta masa ya mika takardarsa ta asusun ajiyarsa na banki domin tabbatar da an kididdige duk wani kudaden shiga da fita da kuma hana sayen kuri’u musamman a ranar zabe.
Ya kuma bayyana cewa, wannan tsari shi ne na dukkan bangarorin tattalin arziki don tabbatar da daidaito da gaskiya.