By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Alhamis ne ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara suka kada kuri’ar amincewa da tsige mataimakin gwamnan Mahdi Gusau.
Matakin da majalisar ta dauka na tsige shi ya biyo bayan kudirin da mataimakin shugaban majalisar kuma shugaban kwamitin kula da asusun gwamnati, Musa Yankuzo ya gabatar, kuma Yusuf Maru ya amince da shi.
Bayan da kudirin ya koma a karo na biyu, shugaban majalisar, Nasiru Magarya, ya umurci magatakardar majalisar, Shehu Anka, da ya tabbatar da zaben kowane dan majalisar da ya halarci zaman majalisar kamar yadda doka ta tanada.
‘Yan majalisar 18 daga cikin 22 ne suka kada kuri’ar amincewa da tsige shi.
Jim kadan bayan kammala kada kuri’ar, shugaban majalisar ya ce, “Bayan cika sharuddan da dokar ta tanada, majalisar ta zartar da wani kakkarfan kudiri na neman babban alkalin jihar, Mai shari’a Kulu Aliyu, da ya gaggauta kafa kwamitin da zai binciki dukkan zarge-zargen da ake yi wa Mataimakin Gwamna. Mahdi Aliyu Muhammad Gusau, kamar yadda yake kunshe a cikin tanadin sashe na 188 (5) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da aka yi wa kwaskwarima.”
A zaman da aka yi a ranar Laraba, shugaban majalisar ya ba da umarnin a ba wa kowane dan majalisar takardar tsige shi tare da duk wasu zarge-zargen da ake yi masa na la’akari da matakin da ya dace.
Da wannan ci gaba, hankali ya koma ga babban alkali ya kafa kwamitin da zai binciki mataimakin gwamna kamar yadda dokar kasa ta tanada.