Hukumar hana zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Kaduna KASTLEA, ta umarci jami’anta da su dakatar da ci gaba da kafa shingayen binciken ababen hawa a fadin jihar.
An kuma hana jami’an na KASTLEA rike sanduna kowane iri a yayin gudanar da ayyukan su.
An sanar da matakin ne a wata takarda da hukumar ta fitar Kuma ta rabawa dukkan kwamandojin shiyya na KASTLEA mai dauke da sa hannun shugaban sashin gudanarwa, Aliyu Manga.
Sanarwar ta ranar 7 ga Fabrairu, ta zo ne kwanaki uku bayan da Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani mataimakin direba ya mutu a wata hatsaniya da jami’an KASTLEA a garin Kaduna .
Wadanda suka shaida lamarin sun ce an yi jami’an hukumar ne suka daki direban da sanda a lokacin da takaddama ta barke a tsakanin su, inda daga bisani ya mutu a asibiti.
A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kaduna (CP), Mudasiru Abdullahi, ya bayar da umarnin damke jami’in da ake Zargi da aikata wannan mummunan aiki.