Jami ‘an Rundunar Ƴan Sandan Najeriya sun kama wani Kehinde Adejumoke Oladimeji ɗan shekaru 43 da Matar shi Adejumoke mai shekaru 35 da zargin mallakar sassan jikin mutum.
Ma’auratan suna zaune ne a gida mai lamba 72 MKO Abiola dake kan hanyar Leme Abeokuta, cikin Ƙaramar Hukumar Abeokuta ta Kudu a Jahar Ogun.
Wani wakilin Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ya ruwaito cewar an kama su ne biyo bayan rahoton da aka samu a hedkwatar ƴan sanda ta Kemta daga wani Chief Moshood Ogunwoluz Shugaban Al’ummar Leme.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zuwan jami’an INEC a makare yana kawo jinkirin a zaben FCT
Baale ya shaidawa ƴan sanda cewa Fasto Adisa Olarewaju ya sanar dashi wani mummunan wari dake fitowa daga ɗakin wanda ake zargin.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Abimbola Oyeyemi a ranar Talata ya shaidawa manema labaru cewa bayan bada ƙorafi CSP Adeniyi Adekunle ya jagoranci jami’ai zuwa wurin gudanar da bincike