By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta dakatar da wasu ‘yan sanda biyu bisa zarginsu da hannu a safarar miyagunb kwayoyi.
Jami’an,sun hada da Sunday Ubua, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (ACP) da James Bawa, mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP) an mika su ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA domin gudanar da bincike.
Mista Ikechukwu Ani, shugaban yada labarai da hulda da jama’a na hukumar ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Ani ya ce jami’an na aiki ne a karkashin mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar (DCP), Abba Kyari, wanda shi a yanzu haka aka kama shi tare da kuma mika shi ga hukumar NDLEA bisa wannan zargi.
Kyari dai shi ne Kwamandan Sashen Bincike da Leken Asiri na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriyar, kafin a dakatar da shi.
An dakatar da Kyari ne biyo bayan tuhumar da hukumar bincike ta tarayya ta yi masa.
Ani ya ce dakatarwar da aka yi wa jami’an biyu ta fara aiki nan take, ya kuma kara da cewa matakin na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikewa babban sufeton ‘yan sanda, mai kwanan wata 16 ga watan Fabrairu.
Ya ce wasikar tana dauke da sa hannun mai shari’a Clara Ogunbiyi, mai ritaya na kotun koli da kwamishina 1 shugaban hukumar Alhaji Musiliu Smith.
Ani ya ce wasikar mai taken: “Sake binciken kamawa tare da mika wa NDLEA kilogiram 25 na hodar ibilis daga ofishin DCP, na (IRT) a ofishin ‘yan sandan Najeriya.
An ci gaba da cewa, “Hukumar a bisa tanadin dokar ma’aikatan gwamnati mai lamba 030406, ta amince da dakatar da jami’an har sai an kammala bincike kan zargin da ake yi musu.
“Hukumar ta kuma umurci Sufeto Janar na ‘yan sanda da ya lura cewa Kyari, wanda kafin wannan zargi ya dakatar da shi, zai ci gaba da kasancewa har sai an kammala bincike.
“An bukaci Sufeto-Janar na ‘yan sandan da ya dakatar da shi, Insp. Simon Agrigba da Insp. John Nuhu bisa ga Ikon Tawagar.”
A cewar sanarwar, an kuma bukaci I-G da ya sanar da hukumar game da kama John Umoru, mataimakin Sufeton ‘yan sanda wanda a halin yanzu yake hannun riga domin daukar matakan da suka dace.
Kazalika Ani ya ce hukumar ta umurci hukumar ta I-G da ta bata bayanai kan ci gaban da aka samu kan lamarin domin ci gaba da daukar mataki.