Kungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi ta Kasa (ASUP) ta bukaci mambobinta a makarantun kasar Nan, da suka kasance cikin shiri domin kuwa kowane lokaci daga yanzu zasu iya Jin Kira domin Tsunduma Yajin Aiki.
Shugaban Kungiyar na Kasa Mr Anderson Umezurike Ezeibe shine ya sanar da hakan yau, yayin ganawa da manema labarai a Kwalejin Fasaha ta Gwamnatin Tarayya dake Kazaure, a Jihar Jigawa.
Mr Anderson ya ce daga cikin abubuwan da suka cimma matsaya da Gwamnatin tarayya, a Watan Yunin da ya gabatar na shekarar Bara. Har yanzu Gwamnatin tarayya ta gaza aiwatar da yawa daga cikinsu.
Idan za a iya tunawa kungiyar ASUP ta janye Yajin Aikin da ta fara a ranar Q0 ga watan Yunin Bara, sakamakon cimma matsaya da su Kai da Gwamnatin tarayya.