Jam’iyyar APC mai mulki ta ware mukamin shugaban ta ga yankin Arewa gabanin zaben shekarar 2023.
Gwamna Nasiru El-Rufai (Kaduna) da Atiku Bagudu (Kebbi), ne suka bayyana hakan a lokacin da suke amsa tambayar wakilin Jaridar Daily Trust a wani taron manema labarai da suka gudanar bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jam’iyya mai mulki.
El-Rufai ya ce jam’iyyar ta amince da sauya mukaman da za’a ba kowa a cikin kwamitin ayyuka na kasa (NWC) a tsakanin sassan Arewa da Kudancin kasar nan gabanin babban taron kasa na ranar 26 ga Maris.
“Idan dai za a iya tunawa cewa, mukamin shugaban jam’iyar wanda tsohon Gwamna John Odigie-Oyegun da Adams Oshiomhole na Jihar Edo daga Kudu suka rike, yanzu zai koma yankin Arewa.” Inji shi
El-Rufai ya ce, “Mun amince da tsarin shiyya-shiyya na rarraba Mukaman siyasa ga shiyyoyi s guda shida da muke da su a kasar nan, kuma mun yi musanya da su. Shiyyoyin Arewa za su dauki mukaman da shiyyar Kudu ke da su a shekaru takwas da suka wuce, akasin haka.
“Don haka, tsari ne mai sauqi qwarai, daidaito da adalci. Yanzu za mu koma mu tuntuba a matakin shiyya, mu duba mukaman da ake da su kuma za a fara shirye-shiryen taron da gaske. Don haka da yardar Allah ranar 26 ga Maris za mu yi babban taron mu na kasa.”
Takaitaccen taron da ya gudana a zauren majalisar dokokin fadar shugaban kasa a Abuja ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnoni 19 da suka hada da na Gwamnannonin jihohin Yobe, Kano, Kogi, Ekiti, Nasarawa, Kwara, Ebonyi, Jigawa, Lagos, Imo. Ogun, Borno, Niger, Gombe, Osun, Kebbi, Plateau, da kuma mataimakin gwamnan jihar Anambra wanda ya bar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) zuwa APC a bara.