Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyar sa ga masarautar Kazaure da ke jihar Jigawa bisa rasuwar Alhaji Ilyasu Adamu, Tafidan Kazaure.
Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Garba Shehu ya fitar, ya bi sahun masarautar da iyalan Adamu wajen addu’ar Allah ya jikan Marigayin.
Alhaji Iliyasu Adamu Wanda Mai rasuwa ya kasance mataimakin darakta mai kula da harkokin walwalar jama’a a ma’aikatar lafiya da ci gaban jama’a ta jihar Jigawa.
‘’Ayyukan jin kai da Marigayi Tafidan Kazaure ya yi sun sa jama’a su kaunace shi, kuma mutanen da suka yi mu’amala da shi kai tsaye za su yi kewar sa a Jihar Jigawa da sauran su.
Duba Wannan: https://dimokuradiyya.com.ng/covid-19-ta-kashe-yan-najeriya-3000-a-cikin-shekaru-biyu-ncdc/
“Allah ya ba shi Jannatul Firdaus,” in ji shugaba Buhari a sakon ta’aziyyar sa.