Tsohon shugaban masu tada kayar baya a yankin Neja Delta Asari Dokubo yayi barazanar kashe Shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu.
Dokubo ya yi barazanar kashe Kanu a cikin kotun da hannunsa.
Tsohon shugaban rusasshiyar kungiyar Movement for the Emancipation of Niger-Delta ya yi wannan barazanar ne yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa wasu ‘yan kungiyar IPOB sun yi masa duka.
Da yake watsi da irin wadannan ikirari, Dokubo ya ce ranar da irin haka ta faru, a zahiri zai garzaya kotu ya kawar da shugaban kungiyar ta IPOB da kansa.
A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dokubo ya bayyana irin wannan ikirarin a matsayin karya.
“Kuna iya tunani o, Za ku iya magana, amma a ranar da kuka gwada duk wannan karyar da kuke yi, a zahiri zan je na kashe Nnamdi Kanu ko da a kotu, har ma da sojojin Najeriya da duk jami’an tsaron Najeriya da ke kewaye da shi”
“Ba zan aika kowa ba, zan je can in kashe shi da hannuna,” in ji shi.
Rikicin Yan Neja-Delta da magoya bayan Nnamdi Kanu ya yi tsami tsawon shekaru ma su yawa.
Kanu na fuskantar tuhuma kan ta’addanci a gaban mai shari’a Binta Nyako a babbar kotun tarayya da ke Abuja