By Abbas Yakubu Yaura
Wasu daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba su samu shiga kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar APC mai mulki ba.
DUBA WANNAN LABARIN: Masarautar Gaya Zata Hada Hannu Da Jami’an Kula Da Zirga-zirgar Ababen Hawa
A babban taron jam’iyyar, wanda aka gudanar a dandalin Eagle Square, a ranar Asabar, an maye gurbin akalla hudu daga cikin ‘yan takarar da suka samu goyon bayan shugaban kasa kafin gudanar da babban taron.
Amma Sanata Abdullahi Adamu, wanda ke kan gaba a jerin ‘yan takarar da shugaban kasa ya tantance ya samu mukamin shugaban Jam’iyyar.
Tun kafin a fara taron mutane shida ne suka ajiye masa takarar inda Sanata Sani Musa daya daga cikinsu ya amince cewa yanke shawara ce mai matukar wahala.
A wata takarda mai shafuka 12 da aka yada a farkon taron, gwamnonin jam’iyyar 22 sun bayyana sunayen mutane 78 na mukaman kasa da na shiyya.
Wadanda wannan mataki na gwamnonin ya shafa sun hada da:
Mutanen hudu an ba su sunayen mataimakan shugabannin jam’iyyar na yankin (Kudu), mataimakin shugaban Jam’iyyar na kasa yankin (Arewa), sakatare na kasa da kuma sakataren tsare-tsare.
A madadin su gwamnonin sun zabi Cif Emma Enuekwu, Sanata Abubakar Kyari, Sanata Iyiola Omisore, da Suleiman M. Argungu.
Masu adawa da mutanen hudu sun tabbatar da labarin musamman na Jaridar Daily Trust a ranar Laraba, wanda ya rawaito makircin da gwamnoni da wasu sarakuna suka yi na kawar da wadanda shugaban ya nada.