Jakadan Nijeriya a kasar Jamhuriyyar Benin, wato Kayode Oguntuase, ya tabbatar da cewa ba a kai wa ofishin Nijeriya a kasar hari ba, sabanin rahotannin da ake yadawa a shafukan sada zumunta.
Ofishin Jakadancin Nijeriya ya tabbatar da hakan ne ga kamfanin dillancin labaran Nijeriya a ranar Lahadi, inda suka tabbatar da cewa labarin karya ne kawai aka yada.
Ya ce tun bayan yada labarin, ake kiran ofishinsu dake Kwatano ta waya domin tabbatarwa. Ya ce bidiyon da ake yadawa cewa ofishin ne aka kai wa hari, sam ba gaskiya bane.
Ya tabbatar da cewa huldar Jakadancin Nijeriya da jamhuriyyar Benin, na nan daram ba tare da wata matsala ba.