Kasar Rwanda tace, ta na matukar bukatar Karin wasu Makudan kudade domin cigaba da aje dakarunta a yankin Cabo Delgado na arewacin Muzambique, inda suke yaki da masu Ikirarin jihadi.
A dai shekarar da ta gabata ne, Rwanda ta tura dakarun sojin ta guda dubu guda, inda suka yi nasarar kwace wasu kauyuka da biranen daga Mayakan dake ikirarin jihadi.
Jakadar Rwanda a Mozambique ya ce, kasar ta bukace kungiyar tarayyar Turai da ta tallafamata domin tabbatar da komai ya dai daita a yankin.
Kana ya cigaba da cewa, akwai wasu Karin cigaba da dakarun kasar suka samu tun bayan aikin wanzar da zaman lafiyar da suka fara.
Ya Kuma kara da cewa, haryanzu babu Wani wa’adi da aka tsara na zaman da Sojojin Rwandan keyi a yankin.