Ana gudanar da taron koli tsakanin kasashen Isra’ila, Masar, Maroko da kuma wasu kasashen Larabawa biyu a Negev dake kasar Isra’ila.
Sakataran kula da harkokin kasashen waje na Kasar Amurika Antony Blinken na daya daga cikin mahalarta taron Wanda ake kyautata zaton cewa, zai mai da hankali ne kan Kudirin Iran na makamashin Nokiliya, da kuma batun yakin Ukraine da Rasha.
Ministocin kasashe irin su Masar, Daular Larabawa, Maroko da kuma Bahrain sun halarci taron dake Gudana a Isra’ila, a wani yunkuri na karfafa alakar su da Isra’ila.
Kazalika kasashen sun kuma yi Allah wadai da mummunan harin da aka Kai a Isra’ila ranar Lahadi da yayi sanadiyar mutuwar wasu jami’an yan sanda biyu.