Gwamnan jihar Nasarawa, wato Abdullahi Sule ya bayyana cewa; duk wanda aka zaba a matsayin gwamnan jiha ba shi da hurumin satar kudin al’umma. Kuma idan har aka kama gwamna ya saci kudin al’umma, to tabbas shaidani ne.
Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayani a musabakar karatun Alkur’ani na kasa karo na 23 na Kungiyar Izala bangaren Jos wato JIBWIS Jos da ya gudana a ranar Asabar a garin Lafia.
A cewarsa, duk zababben gwamna da aka kama yana satar kudin al’umma, tabbas yana da bukatar addu’a. Inda ya kara da cewa; gwamnoni an samar musu da yanayin da ba su da bukatar su saci dukiyar al’umma, ya ce; amma duk gwamnan da aka kama yana satar dukiyar al’umma, to tabbas shaidani ne.