Kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya ta Super Eagles ta rike wa ta Brazil wuya a wasan sada zumunta da suka buga a filin wasa na The National Stadium na kasar Singapore, inda wasa ya tashi kunnen doki wato 1-1.
A iya cewa kungiyar ta Super Eagles da kyar ta sha domin kuwa Brazil ta fi ta taka kusan kowacce irin rawa a wasan.
Nijeriya ce ta fara jefa kwallo a raga ta hannun Joe Aribo a minti na 35, inda ya kutsa tsakiyar ‘yan bayan Brazil bayan Simon ya ba shi kwallon a cikin yadi na 18 – sai da ya yanke mutum biyu kafin ya tsula ta cikin raga.
Casemiro ne ya farke wa Brazil tata kwallon a minti na 48 bayan kwallon da Marquinhos ya saka wa kai ta bugo turke ta dawo, inda shi kuma Casemiro ya yi azama ya buga ta cikin raga.
Wasa na uku ke nan a jere da Brazil ta buga ba tare da nasara ba biyo bayan kashin da ta sha a wasannin sada zumunta a hannun kasar Peru da ci 0-1 da kuma canjaras tsakaninta da Kwalambiya duka a watan Satumba.
Ita kuwa Nijeriya wasanta na farko ta buga ke nan tun bayan nasarar da ta samu a kan Tunisiya da ci 1-0 a wasan neman na uku a gasar cin Kofin Kasashen Afirka na 2019.