By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an tsaron Najeriya da rundunar tsaro ta farin kaya NSCDC ta jihar Jigawa ta tabbatar da cewa mutane bakwai ne suka mutu a wata gobara data kama a wani gidan mai dake Al-Masfa a karamar hukumar Kaugama ta jihar.
DUBA WANNAN LABARIN: 2023: Malami Ya Bayyana Aniyar Sa Ta Tsayawa Takarar Gwamnan Jihar Kebbi
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Mista Adamu Shehu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a Dutse ranar Talata, ya shaidawa manema labarai cewa har zuwa lokacin hada rahoton ba a iya gano musabbabin tashin gobarar.
Shehu ya bayyana cewa, an yi hadin gwiwa da jami’an kwana-kwana da jami’an tsaro wajen kashe gobarar.
“Gobarar ta kone wani gini da ke zama shingen gudanarwa da kuma wurin kwana ga ma’aikatan gidan man.
“Abin takaici, wasu daga cikin wadanda abin ya shafa na barci yayin da wasu ke hutawa bayan gajiyawar aikin ranar.
“Sakamakon haka, shida daga cikin wadanda abin ya shafa sun mutu nan take yayin da daya yace gagarin kunan bayan an kai shi asibiti.”
Ya bayyana sunayen marigayin da Nasiru Umar mai shekaru 30; Abdulkadir Nura mai shekaru 25; Dahawi Garin-Babale mai shekaru 35; Hamza Adamu mai shekaru 15; Sulaiman Garin-Babale mai shekaru 35; Idris Adamu mai shekaru 40; da Salisu Garin-Babale mai shekaru 40.
NAN
Comments 1