By Abbas Yakubu Yaura
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF), Abubakar Malami, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kebbi a shekarar 2023.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Cross River Ta Musanta Zargin Rashin Kin Biyan Albashin Ma’aikata A Jihar
Malami ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar a wani taron da aka gudanar a Kebbi ranar Litinin.
Ya rasa tikitin takarar gwamnan jihar Kebbi a hannun Atiku Bagudu na jam’iyyar APC, wanda a halin yanzu yake gwamnan jihar tun a shekarar 2014.
Yanzu dai Bagudu na shirin kammala wa’adin mulkin sa na biyu.
“Allah cikin rahamar sa, kuma komai ya daidaita, ni a matsayina na dan siyasa zan tsaya takarar Gwamnan Jihar Kebbi. Ina neman goyon bayan ku.
“Ina so in sanar da cewa lallai zan tsaya takara kuma a saboda haka ina dogara da addu’o’in ku da goyon bayan ku domin mu yi aiki tare kuma mu tsira tare.
Ba ni da tarihin cin amana kuma ba zan ci amanar ku mutane ba. Zan yi muku aiki,” kamar yadda jaridar Thisday ta ruwaito Malami yana cewa.
Comments 2