Sakataren APGA na Ƙasa, Labaran Maku ya koma PDP
Labaran Maku, Sakataren Jam’iyar APGA na Ƙasa, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyar PDP.
Maku, tsohon Ministan Yaɗa Labarai a lokacin mulkin Jonathan Goodluck, ya baiyana komawar tasa PDP ne ga Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN a jiya Talata a garin Lafia.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani yakai ziyara girmamawa ga Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya nemi Tabarraki
Ya ce ya ɗauki matakin koma wa PDP ne domin ya amsa kiraye-kirayen da al’ummar Jihar Nassarawa ke yi masa.
A tuna cewa a 2015 ne .Ali ya sauya sheƙa da ga PDP zuwa APGA da nufin samun tikitin takarar gwamna a jihar.
Sannan ya yi takarar gwamna sau biyu a jam’iyar APGA ɗin a shekarar 2015 da 2019, amma duk bai samu nasara ba.
Comments 1