Rundunar atisayen ‘Thunder Strike’ a Kaduna sun ‘yanto wadansu manoma uku daga hannun ‘yan bindiga da aka yi garkuwa da su. Rundunar ta ce manoman an sace su a ranar Laraba a kauyen Maro dake kan titin Kaduna zuwa Abuja.
Mataimakin Daraktan Hulda da jama’a na rundunar soja ta I dake Kaduna, Kanal Ezindu Idimah shi ne ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Nijeirya hakan a Kaduna, inda ya tabbatar da cewa; sun kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutanen a yayin samamen da suka kai.
Ya kara da cewa; sun kai samamen ne bayan sun samu bayanan sirri, inda suka kai ma maboyar ‘yan bindigar hari wanda ya kai sai da suka yi musayar wuta a tsakaninsu, inda ya ce a karshe sun yi nasara kan ‘yan bindigar inda suka gudu da raunuka a jikinsu tare da barin wadanda suka yi garkuwa da su.
Ya tabbatar da cewa; tuni suka mika wadanda suka ‘yanto ga iyalansu. Inda kuma ya ce sun samu nasarar kwace bindiga kirar Ak 47 da kuma wadansu kwanson harsasai.