Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kame wasu kadarori na dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sandan Abba Kyari, a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Majiyar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa umurnin ya fito ne daga hedkwatar hukumar, da ke cewa duk kadarorin naKyari ne, wanda ya fito daga Borno, kuma yanzu haka yake tsare tun watan Fabrairu lokacin da aka kama shi tare da wasu mutane shida bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar NDLEA ta sanar da kama wani hamshakin attajirin nan mai suna Cif Afam Mallinson Emmanuel Ukatu da ake zargi da hannu wajen cinikin tramadol na N3bn da ya shafi Kyari.
A cewar mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi, an kama Ukatu ne a Abuja bayan shafe watanni ana sa ido akan shi.
A binciken hukumar NDLEA da ya shafi Kyari a Maiduguri, yanzu haka dai rahotanni sun bayyana cewa tuni hukumar ta fara bincike kan wasu katafaren shaguna kusan 100.
“Eh, mutanen mu sun gudanar da aikin ne kamar yadda hedkwatar ta umarta, ba kawai rukunin gidaje ba akwai wasu gidaje mallakin DCP Abba Kyari amma idan kuna son karin bayani a tuntubi kakakin hukumar mu,” inji wani jami’in hukumar.