Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya rubuta wasika zuwa ga shugaban jam’iyyar APC Sen Abdullahi Adamu.
Cikin wasikar dai Marwa ya bukaci a baiwa jami’an NDLEA damar gudanar da gwajin taammali da miyagun kwayoyi.
Gwajin shan kwayoyi zai gudana ne tsakanin ‘yan siyasa masu neman mukamai a zaɓen dake tafe a 2023.
Marwa ya ce a lokacin da PDP da sauran jam’iyyu za su gudanar da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar, zai kuma rubutawa shugabannin jam’iyyar na kasa ya kuma bukaci jami’an NDLEA su gudanar da gwajin ingancin kwaya ga ‘yan siyasa masu neman mukamai.
Shugaban hukumar ta NDLEA wanda ya ke jawabi a wajen bikin karramawar Kwazon na 1 na hukumar a Abuja ya bayyana cewa gwajin magungunan ya zama dole don tabbatar da cewa ‘yan siyasa masu rike da muhimman ofisoshin kasa ba su yi amfani da kason kasafin kudi ba wajen sayen hodar iblis ko makamantansu ba, maimakon samar da ayyukan da ake bukata. ga talakawan kasa.