By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta ce ta sake tura jami’anta kusan 4,000 domin tabbatar da tsaro yayin gudanar da bikin Sallah da ke tafe.
Wannan tura jami’an ya biyo bayan barazanar da ‘yan ta’adda suka yi na kai hare-hare a wasu sassa daban daban na jihar.
Ku Duba Jinjirin Watan Shawwal A Ranar Asabar, Sultan Ya Fadawa Al’ummar Musulmin Najeriya
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abimbola S. Sokoya, ya bayyanawa manema labarai a ranar Juma’a cewa: “Mun riga mun tura mutanenmu, kuma za mu tura jami’an ‘yan sanda sama da 4000.”
Da yake yiwa mazauna yankin alkawarin gudanar da bukukuwan Sallah ba tare da wata tangarda ba, ya bukaci jama’a da kada su yi kasa a gwiwa wajen jawo hankalin jami’an tsaro kan duk wani yunkuri na shakku a yankunansu.
Ya nemi hadin kan jama’ar jihar yana mai cewa ‘yan sanda sun zo nan don baiwa mazauna jihar tabbacin cewa za mu sake fasalin gine-ginen tsaro, ya kamata dukkan su su amince da mu.
Ya ce ‘yan sanda sun gano cewa “wadanda suka aikata laifuka a jihar sun samu hadin gwiwar wasu daga waje” inda ya kara da cewa “saboda ’yan Taraba mutane ne masu son zaman lafiya, kuma ba shakka ba za su yi irin wannan aika-aika da abin kyama ba.
Har ila yau da yake magana kan tashin bama-bamai da suka faru a jihar a lokuta biyu, ya ce ‘yan sanda sun tsara hanyoyin da za su dakile aukuwar lamarin nan gaba.
Idan dai zaku iya tuna cewa gwamnan jihar, Darius Dickson Ishaku, ya bayar da umarni ga jami’an tsaro kan bukatar su tabbatar da ziyartar otal-otal, gidajen karuwai, wuraren shan giya, wuraren shakatawa, wuraren shakatawa na motoci, kasuwanni da sauran su domin kawar da miyagun laifuka.
Kwamishinan wanda ya amince da cewa hukumar ta aiwatar da wannan umarni, ya ce an rage yawan laifuka a jihar zuwa mafi karanci.
Comments 1