By Abbas Yakubu Yaura
A yayin da watan Ramadan na shekarar 1443 (2022) ke kawowa karshe, Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), karkashin jagorancin Shugabanta Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bukaci al’ummar Musulmi a fadin Najeriya dasu fara duban jinjirin watan Shawwal a ranar Asabar.
Daraktan Gudanarwa na NSCIA, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin Sarkin Musulmi a ranar Juma’a.
Ya ce sakamakon shawarar da kwamitin ganin wata na kasa (NMSC) ya bayar, Sarkin Musulmi ya bukaci al’ummar Musulmin Najeriya da su nemi jinjirin watan Shawwal 1443 bayan faduwar rana a ranar Asabar 30 ga watan Afrilu, 2022, daidai da 29 ga watan Ramadan shekarar 1443 AH.
“Idan Musulmi suka ga jinjirin watan, mai martaba Sarkin Musulmi zai bayyana Lahadi 1 ga Mayu, 2022, a matsayin 1 ga Shawwal da ranar ‘Idul Fitr. Koyaya, idan ba a ga jinjirin watan a wannan ranar ba, to Litinin 2 ga Mayu 2022, kai tsaye ta zama ranar ‘Idul Fitr’.
DUBA WANNAN LABARIN: Falasdinawa Da Dama Ne Suka Jikkata A Arangamar Da Sukayi Da ‘Yan Sandan Isra’ia A masallacin Kudus
“Baya ga shugabannin addinin Musulunci da aka kafa da kuma na gargajiya a kowace karamar hukuma, ana iya tuntubar mambobin NMSC don bayar da rahoton ganin jinjirin watan Shawwal 1443 AH,” Usman-Ugwu ya ce.
Ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su ci gaba da azumin watan Ramadan, su tuna cewa zakkatul Fitr (zakata musamman na watan Ramadan) wani harajin abinci ne na wajibi da aka dora wa musulmi masu gata, don baiwa marasa galihu a cikin al’umma.
Don haka ya bukaci duk wanda abin ya shafa da su tabbatar ba sun aiwatar da ita a kan lokaci.
Ya ce, “Aikin gama-gari shi ne bayar da ma’auni ga masu cin gajiyar a cikin kwanaki biyu na karshen watan Ramadan ba a wucewa kafin sallar idi ba ga wanda yake da ikon yi.
Sarkin Musulmi Abubakar, wanda ya taya al’ummar Musulmin Nijeriya da ma daukacin al’ummar Musulmin duniya baki daya murnar zagayowar shekarar Hijira ta 1443, ya yi addu’ar Allah ya ba kowa damar shaida da yawa daga cikinsu.
Ya kuma bayyana damuwarsa kan hauhawar farashin kayan masarufi a kasar nan, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kawo karshen hauhawar farashin kayayyaki yayin da ya kuma bukaci ‘yan kasuwa da su daina dabi’ar kara farashin kayayyakin abinci ba gaira ba dalili.
Comments 1