Kotun Majistare a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Babban Majistare Aminu Gabari ya bada belin tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin-hanci ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar ‘Yan Sandan Taraba Ta Tura Jami’ai 4,000 Don Samar Da Tsaro Yayin Gudanar Da Bukukuwan Sallah
A jiya Alhamis ne dai ƴan sanda ɗauke da makamai su ka kama Rimingado a masaukin gwamnatin Jihar Sokoto da ke Abuja yayin da ya je tantanc wa ta takarar gwamna da zai tsaya a ƙarƙashin jam’iyar PDP a Kano.
Da ga nan ne ƴan sandan sun ka kai shi shelkwatar ƴan sanda ta Abuja, daga bisani kuma a ka yo Kano da shi domin gurfanar da shi a gaban kotu.
Ana tuhumar Rimingado da bada bayanan ƙarya, laifin da ya saba da sashi na 149 na dokar laifuka ta jihar Kano ta 2019.
Da ya ke ƙwarya-ƙwaryar hukunci a kan rokon bada belin Rimingado, Gabari ya bada belin a kan Naira dubu 500 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa, wanda ɗaya daga cikin su dole ya zama mahaifinsa ne, dayan kuma baffansa, sannan ya kawo sahidar biyan haraji ta shekaru uku.
Sannan kotun ta umarci Rimingado da ya kawo fasfo ɗin shi na tafiye-tafiyen kasashen waje zuwa ofishin Babban Rijistara na Kano, ya kuma kawo Limamin Masallacin Sharada, ko Mai Gari ko Mai Unguwar Sahrada.
Comments 1