Rahotanni daga kasar Sipaniya sun ce Real Madrid ta soma tuntubar tsohon kocinta Jose Mourinho domin sake kulla yarjejeniya da shi, don maye gurbin Zineden Zidane.
Labarin da jaridar El Chiringuito ta labarto, ya zo ne kwana guda bayan da Zidane ya ce yawaita sukar salon horaswarsa da ake yi gami da yada jita-jitar Mourinho zai maye gurbinsa yana ci masa tuwo a kwarya.
Tun bayan sallamarsa da Manchester United ta yi a watan Disambar bara, zuwa yanzu Mourinho ya yi watsi da tayin kulla yarjejeniya da kungiyoyin da suka hada da Benefica da kuma Lyon.
A karshen makon da ya kare, Real Madrid ta sha kaye a hannun Real Mallorca da kwallon 1 mai ban haushi, abin da ya haifar da shakku kan dorewar aikin Zidane, wanda tun bayan sake karbar jagorancin kungiyar ta Madrid, al’amuranta suka gaza komawa kamar lokacin da ya jagorance ta wajen lashe kofunan gasar zakarun Turai uku a jere.