Ministan tsaron kasar Sri Lanka ya bayar da umurnin bude wuta a kan masu tarzoma da ke wawashe ko barnata dukiyar jama’a, bayan da masu zanga-zanga suka fara afka wa gidajen ‘yan siyasa da kuma sauran manyan jami’an gwamnatin kasar.
Yanzu haka dai an baza dubban jami’an tsaro a kan titunan birnin Colomba, don kawo karshen tarzomar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 8 da kuma raunata akalla 65 ciki har da jami’an tsaro, yayin da aka ruwaito cewa an kona motoci kusan 90.
Firaministan Sri Lanka Mahinda Rajapaksa ya sauka daga mukamin sa sakamakon zanga zangar adawa da gwamnati da ta rikide ta zama tashin hankali, abinda yayi sanadiyar mutuwar mutane 5 cikin su harda Dan Majalisar dokoki, yayin da wasu mutane kusan 200 suka samu raunuka.
Rahotanni sun ce wani dan majalisa Amarakeerthi Athukorala daga Jam’iyya mai mulki ya harbe wasu mutane 2, ciki harda wani matashi mai shekaru 27 da yam utu, kafin daga bisani shima ya kasha kan sa lokacin da masu zanga zangar suka masa kawanya.
A wani labarin na daban.
Jigawa: Ƴan Majalisu sun kori Shugaban Ƙaramar Hukuma kan Ƙin Biyayya ga Shugaban APC
Majalisar Dokokin Jahar Jigawa ta kori Shugaban Ƙaramar Hukumar Yankwashi ta Jahar sakamakon zargin yaƙi yin biyayya ga Shugaban Jam’iyyar APC.
Shugaban Kwamitin Majalisar akan Yaɗa Labaru dake wakiltar Kafin Hausa Muhammad Na’im ya bayyana haka ga Manema labaru.
Yace Shugaban Ƙaramar Hukumar an kore shine saboda faɗin maganganu marasa tushe da kuma yaɗa labarin ƙarya akan Shugaban Jam’iyyar APC na Jahar Aminu Ahmed.
A cewar sa “Majalisar ta karɓi ƙorafi daga Shugaban Jam’iyyar APC yana ƙalubalantar Shugaban Ƙaramar Hukumar kan yaɗa labarun ƙarya cewa Shugaban Jam’iyyar yana karɓar kuɗaɗe ga wasu ƴan takara domin yi masu alfarma.
Ya bayyana cewa Majalisar ta kuma daɗe tana karɓar ƙorafe-ƙorafe kan lalata Dukiyar jama’a da Shuwagabannin Ƙananan Hukumomi guda 8 ke yi.
“Majalisar ta kafa wani kwamiti domin yayi bincike kan Shuwagabannin Ƙananan Hukumomi guda 8 da suka haɗa da Gwaram, Kafin Hausa, Guri, Miga da Birnin Kudu, da Birniwa, da Babura”, Inji shi.
Wani daga cikin Shuwagabannin Ƙananan Hukumomin wanda ya buƙaci a sakaye sunan sa ya bayyana cewa, zargin Ƙarya ne, bai faru ba.
Yace zargin kawai ba komai bane illa irin na Siyasa.
Comments 1