Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa bata damu da kalaman da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar inda ya yi ba, inda yake ikirarin cewa ba zai goyi bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba a 2023 ko da kuwa za a bashi damar taimakon nasa.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammad Garba ya fitar ta bayyana cewa, rashin goyon bayan Gwamna Ganduje, hakan na nufin cewa Farfesa Abubakar ba zai goyi bayan jam’iyyar da yake cikinta ba wato APC.
Kazalika gwamnati ta bayyana mamakinta da irin wadannan kalamai na rashin yabo, a don hK ne sai yayi addu’ar Allah ya dawo masa da hankalinsa domin ya goyi bayan jam’iyyarsa ta siyasa.
Sanarwar ta kara da cewa, a baya-bayan nan ne a wani faifan bidiyo da Farfesa Abubakar ya yi wa dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna, sa mataimakin sa Murtala Sule Garo, kalaman cin fuska da cewa kamata yayi ace suna a gidan gyaran hali a garkame maimakon tsayar da su domin takara.
Malam Garba ya bayyana cewa idan da gaske shi dan jam’iyyar APC ne, jam’iyyar na mutunta goyon bayan da dukkan mambobinta ke ba su don samun nasara ko da matsayinsu.
Ya ce tsohon mataimakin gwamnan ya yi shekara uku a gwamnatin Ganduje har sai da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar (PDP) kuma aka yi masa maraba da komawa jam’iyyar bayan sun yi kaca-kaca da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Kwamishinan ya bayyana cewa hatta ubangidansa na siyasa, wanda shi ne darakta-janar, kungiyar yakin neman zabe, Sanata Barau Jibrin, ya sasanta da gwamnan tare da sake tsayawa takarar Sanatan Kano ta Arewa.
Malam Garba ya ce dangane da abin da ya shafi jam’iyyar APC, zai yi hannun riga da Farfesan da har yanzu a jam’iyyar APC ya bayar da goyon bayansa ga Sanata Ibrahim Shekaru wanda ke sake tsayawa takara a wata jam’iyya ta daban.
Ya ce abin takaici ne yadda a wannan lokaci da jam’iyyar ke kara tabarbarewa bisa la’akari da rigingimun siyasa na baya-bayan nan, kamata ya yi tsohon mataimakin gwamnan ya tunkari duk wanda yake da wata matsala a cikin jam’iyyar maimakon yin kalamai na rashin hankali.
Sanarwar ta yi kira ga tsohon mataimakin gwamnan da ya kiyaye da irin wadannan kalamai duba da matsayinsa na dattijon jiha, mai rike mukamin Farfesa kuma dan jam’iyyar APC.