Wani Dan majalisa jihar Gwambe mai suna Alhaji Mustapha Yakubu, a ranar Litinin ya ba da kyautar Gadon majinyata guda biyar ga wani karamin asibiti a Gwambe ‘Family Support Health clinic.’
Da yake magana a yayin mika Gadejen, Dan Majalisa Yakubu, wanda yake wakiltar Gwambe ta Kudu, ya ce ya ba da kyautar ne bisa neman hakan da karamin asibitin ya yi. Inda ya ce ya kai wa asibitin ziyara ne domin gano irin tallafin da suke bukata, a lokacin da hukumar asibitin suka kawo korafi dangane da matsalolin da suke fuskanta na rashin gadajen majinyata.
Dan majalisar ya ce a yau ya cika alkawarin da ya dauka a lokacin da ya kawo wa asibitin ziyara. Ya tabbatar da cewa zai yi dukkanin mai yiwuwa wajen tabbatar da kayayyakin an bunkasa su zuwa yadda al’umma su amfana.