Wadansu manoman shinkafa sun nemi gwamnatin tarayya da ta tallafa musu ta hanyar ba su bashi wanda zai bunkasa musu noman shinkafa domin rage farashin shinkafar, inda suka bayyana rufe iyakokin kasar da gwamnati ta yi a matsayin abin maraba.
Rahotanni sun bayyana cewa; farashin shinkafa mai nauyin 50kg wacce ake nomawa a gida ana siyar da ita naira 14,000 kafin a rufe kan iyakokin Nijeriya, inda a yanzu ake siyar da shi naira 22, 000 bayan an rufe iyakokin Nijeriya.
Manoman shinkafar, wadanda suka yi kira da a basu wannan bashin sun nemi hakan a yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Litinin a birnin tarayya Abuja, inda suka jaddada cewa yadda ake siyar da shinkafar da ake nomawa a gida a halin yanzu ya yi tsada da yawa.