Sai ka nuna mana inda muka lalata bututun Mai a Najeriya — IPOB ga Buhari
Ƙungiyar Tsagerun Kafa Ƙasar Biafra ta bayyana maganganun da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi cewa ita ke da alhakin lalata bututun da Gwamnati ta sanya a matsayin “abun dariya, abun jin kunya, kuma cikakkiyar ƙarya”.
Ƙungiyar masu fafutukar Kafa Ƙasar ta tunatar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari cewa ƙasashen yamma tuni sun san ko su waye keda alhakin lalata bututun a Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan jihar Kebbi ya amince da kudaden garatuti na naira billiyan 3 ga ma’aikatan jihar
A cikin wata sanarwa daga Sakataren Yaɗa Labaru na IPOB Emma Powerful ya fitar, yace ga Buhari ya gayawa Amurka da sauran Ƙasashen yamma cewa IPOB keda alhakin lalata bututun mai a yankin Niger Delta ya nuna cewa “tunanin sa gajere ne, kuma marar hange akan abubuwan dake faruwa a Ƙasar.
Powerful ya ƙara dacewa Shugaban Ƙasa ya zabi nuna rashin wayewar sa da kasawar Gwamanatin sa wajen haɗa bayanan sirri na ƙwarai akan wannan zargi da yake yi masu.
Ya ƙalubalanci Shugaba Buhari daya nuna wa Duniya inda Ƙungiyar IPOB ta lalata bututun mai a Ƙasar.
Yace “mai yiwuwa Gwamnatin Fulani bata san cewa Ƙasashen yamma ba sakarkaru bane, jahilai, marasa tunani da hangen nesa, kamar yadda yayi tunani, akan wannan jawabi da yayi.
“Shugaban Ƙasa ya kamata yasan cewa Ƙasashen yamma tuni sun san su waye keda alhakin lalata bututun a Najeriya, da wanda suke amfana. Wannan wane irin sarƙaƙiya ne a Najeriyar Buhari.
Comments 1