Daga: Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 17 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka bayan da wasu ‘yan ta’adda suka kai hari a wani wurin hakar ma’adanai da ‘yan kasar China suke gudanarwa a Ajata-Aboki a unguwar Gurmana na karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.
Rahotanni sun ce an kai harin ne da yammacin ranar Laraba inda aka hallaka mutane bakwai da suka hada da ‘yan sandan tafi da gidanka da ke gadin masu hakar ma’adinai da ma’aikata.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/gwamna-matawalle-ya-goyi-bayan-hukuncin-kisa-ga-yan-bindiga-ya-rattaba-hannu-kan-kudirin-dokar/
An ce maharan dauke da nagartattun muggan makamai, an ce sun isa unguwar ne da misalin karfe biyu na rana, inda suka nufi wajen da ake hakar ma’adinai, inda suke bindige duk wani wanda suka gani.
Kwamishinan tsaron cikin gida da jin kai na jihar, Emmanuel Umar, ya tabbatar da faruwar harin a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, sai dai ya ce kawo yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba.
Ya ce, “Gwamnatin Jihar Neja na son tabbatar da cewa a ranar 29/6/2022 da misalin karfe 16:00 na yamma, bisa ga sanarwar da aka samu cewa ‘yan bindiga sun kai hari a wani wurin hakar ma’adinai da ke kauyen Ajata Aboki a gundumar Erena ta karamar hukumar Shiroro tare da hadin gwiwar jami’an tsaro. An tattaro tawagar zuwa wurin domin amsa kiran damuwa.”
Umar ya ce yayin da tawagar jami’an tsaro ta hadin gwiwa suka yi artabu da ‘yan ta’addan, wanda ya yi sanadin asarar rayuka daga bangarorin biyu.
Ya kara da cewa, “Wani adadin ma’aikatan da ba a tantance ba a wurin hakar ma’adinan da suka hada da wasu ‘yan kasar China hudu an ruwaito an sace su.
“Jami’an tsaro sun hada karfi da karfe domin farautar sauran ‘yan ta’adda tare da ceto wadanda suka jikkata ciki har da jami’an tsaro da suka samu raunuka daban-daban an kai su asibitin gwamnati da ke jihar domin yi musu magani.
“Yayin da gwamnatin jihar Neja ke jajantawa shugabannin hukumomin tsaro a jihar da kuma iyalan wadanda aka kashe, gwamnatin jihar ta ba da tabbacin cewa sadaukarwar da suka yi ba zai tafi a banza ba.”
Umar ya ce gwamnatin jihar ta amince da duk kokarin jami’an tsaro na hadin gwiwa da na al’ummomin jihar na ganin an shawo kan matsalar rashin tsaro a wasu sassan jihar.
Sai dai wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cikin kwarin gwiwa cewa “kusan mutane 11 da suka hada da ‘yan sandan wayar tafi da gidanka bakwai da ke aiki a wurin hakar ma’adinan a yayin da jami’an tsaro da wasu ma’aikatan farar hula shida suka rasa rayukansu a harin.”
Ya ce an kai mutane da dama wadanda suka samu raunukan harbin bindiga da dama kuma suna cikin mawuyacin hali, an kai su cibiyoyin lafiya daban-daban domin yi musu magani.
Sani Yusuf Kokki, Co-Convener, Concerned Shiroro Youths, ya kuma shaida wa Jaridar Daily trust cewa an yi garkuwa da wasu ‘yan kasar China da ba a tantance adadinsu ba, yana mai bayyana harin a matsayin mummunan lamari.
Sannan ya koka da cewa “Sace mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare gama gari a yankunanmu. Abin takaici ne cewa an tilasta mana mu zama tare da wannan gaskiyar abin bakin ciki. Ana kashe mu, ana raunata mu, ana yi mana fyade a tsakanin sauran cin zarafin da ‘yan ta’adda ke yi mana.”