Shugaban kasan Nijeriya, Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar abokinshi, wanda ya ke kira “sadauki Tam David-West.”
Shugaban kasar ya yi ta’aziyyar ne a wata takarda da ta fito da sa hannun mai taimaka masa akan harkokin yada labarai, Femi Adesina a Abuja ranar Litinin.
Shugaba Buhari ya ce, malamin, kuma mawallafin littafai da dama: “Yana da halin sadaukarwa da tsayuwa kyam a kan duk abin da ya yarda dashi.”
Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan David-West, mutunen Buguma da masarautar Kalabari dake jihar Ribas da duk wasu masoyan mamacin.
Shugaban kasan ya kuma yi addu’a ga ruhin mamacin, sannan ya nemi wadanda yarda da ra’ayoyin mamacin da su ci gaba daga inda ya tsaya.
Tam Tamunoemi Solaris wanda aka fi sani da Tam David-West ya yi aiki a matsayin tsohon kwamishinan ilimi a tsohuwar jihar Ribas, sannan tsohon ministan man fetur da makamashi a karkashin mulkin Buhari na soja. Tam ya kuma yi ministan ma’adanai, wuta da karafuna a mulkin Janar Ibrahim Babangida.
Ya rasu yana dan shekara 83 a duniya.