Fasto Oyeleke Moses Emmanuel hadi da Ndagila Ibrahim, suna daga cikin mutanen da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su a cikin watan Afrilun wannan shekara, yau sun samu ‘yancin kansu daga dajin Sambisa.
Bayanan da muka samu da safiyar nan, Malamin wa’azin addinin Kiristan tare da ‘yar bautar kasa, wadda aka sani da sunan Abraham Amuta, mayakan sun yi awon gaba da su ne a daidai lokacin da suke kokarin kai kayan jinkai ga ‘yan gudun hijira, daga cocin Living Faith Church da ke garin Chibok a jihar Borno.
Sauran ‘yan mata biyun kuma, wadanda aka sace su din, wadanda binciken mu bai kai ga tantance sunayen su ba, amma wata majiya ta bayyana cewa daliban Sakandiren (GGSS) Askira Uba ne.
Bugu da kari kuma, wannan shi ne karo na biyu wanda gwamnatin jihar Borno da hadin gwiwar sojojin Nijeriya da jami’an tsaron DSS, kungiyoyin bayar da jinkai, musamman Kalthum Foundation suka yi yunkurin bai daya wajen samun nasarar kwato jama’ar daga hannun Boko Haram.
Majiya mai karfi ta shaida mana cewa an karbo wadannan mutanen ba tare da biyan ko sisin kwabo ba, inda ta kara da tabbatar da cewa, “kuma a takaice zan bayyana maka cewa, wannan somin tabi ne wajen kawo karshen wannan lamari, kuma an samu wannan nasara ce ta hanyar tattaunawa ba kuxin fansa ba”.