Kwamitin Uba Sani a Majalisar Dattijai ya tantance Umar Yahaya a matsayin Shugaban Hukumar UFTF
Sanata Uba Sani mai Wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattijan Najeriya kuma Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna ƙarƙashin Jam’iyar APC ya cigaba da aikin sa na kwamitin Majalisar Dattijai gadan-gadan, a ƙoƙarin sa na sauke nauyin dake rataye a wuyan sa.
A ranar laraba ne dai Sanatan tare da membobin Kwamitin, suka tantance Umar Yahaya a matsayin Shugaban Hukumar UFTF.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cikin Kwana 2, Za A Iya Kamo Ƴan Boko Haram Da Suka Tsere — Ali Ndume
Sanatan ne ya bayyana haka a Shafin sa na Twitter.
“A yau ne Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin banki, inshora da sauran cibiyoyin kudi da shugabanta ya yi nasarar tantance, wanda Shugaban Ƙasa ya aiko Mana Umar Yahaya, domin tabbatar da shi a matsayin mataimakin shugaban hukumar kula da asusun bai-daya (UFTF)”.
Uba Sani yace “An yi ma wanda aka naɗa tambayoyi da dama kan kalubalen da tattalin arzikin Najeriya ke fuskanta da kuma gudunmawar da Hukumar Kula da Asusun Tallafin Kudin (UFTF) za ta iya bayarwa wajen kokarin farfado da tattalin arzikinm”.
“Wanda za’a nadan ya nuna matukar fahimta kan muhimman batutuwa, Sharhinsa yayi dai-dai kuma Ba a sami koke ko suka game da wanda Shugaba Buhari ya turo.
Sanata Uba Sani ya miƙa godiya ta musamman ga Majalisar Dattawan Najeriya. Yace “Kwamitin na son miƙa godiyar sa ga majalisar dattawa bisa wannan damar da ta bamu na yin wannan aiki.