FAO, Gwamnatin Borno zasu magance Matsalar ƙarancin Abinci a yankin Arewa maso Gabas
Hukumar kula da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya haɗin gwuiwa da Gwamnatin Jahar Borno sun kaddamar da gurbin noman damina na Manoma 42,000 domin magance matsalar abinci a Jahohi guda uku da ta’addancin Boko Haram ya shafa.
Jami’in Kula da Gaggawa na yankin Arewa maso Gabas a Maiduguri Tofiq Braimah ya bayyana haka a Maiduguri, Jahar Borno cewa kimanin Mutane miliyan 4.1 suna cikin yanayi na matsalar yunwa zuwa watan Disamba a Borno, Adamawa da Yobe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Duk Farfesa zai riƙa ɗaukar Miliyan 2 duk wata, idan Gwamnati ta sanya hannu kan yarjejeniya — Inji Kwamiti
Ya yi nuni dacewar Dabarun Hukumar kula da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya shine inganta samar da Abinci da Noman Damina ga wuraren da rikicin Boko Haram ya shafa.
“Binciken mu ya nuna cewa zuwa watan Disamba na Shekarar 2022, kusan mutane Miliyan 4.1 suna cikin tasku na rashin abinci a Borno, Adamawa, da Jahar Yobe. Samar da abincin rani zai bunƙasa samar da Abinci.
“Muna bada tallafi ga gidajen marasa ƙarfi, ciki har da Ƴan gudun hijira da garuruwansu da kayan Noma domin su sake gina gidajen su. Tallafin lokacin Damina na 2022 zai taimaki gidaje dubu 42,400 a faɗin Jahohin Borno, da Adamawa, da Yobe da Sokoto da Jahar Taraba, daga ciki mutane 19,898 Manoma ne daga Borno kaɗai” Inji Tofiq.
A jawabin sa, Kwamishinan Noma na Jahar Borno Ali Bunu Mustapha ya bayyana damuwar sa na yadda Miliyoyin mutane suna fama da ƙarancin Abinci saboda rikicin faɗa.