Takarar Tinubu-Shettima, yunƙuri ne na Musuluntar da Najeriya — Inji Matasan CAN
Matasan Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya a Jahohi 19 na Arewacin Najeriya da Abuja sun bayyana Takarar Musulmi da Musulmi na Bola Tinubu a Matsayin shedanci da yunkurin musuluntar da Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: FAO, Gwamnatin Borno zasu magance Matsalar ƙarancin Abinci a yankin Arewa maso Gabas
YOWI-CAN ya kuma caccaki Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jahar Filato, Gwamna Simong Bako Lalong, suna cewa kodai ayi wani abu, kuma su tattara matasan su, su shiga zanga-zanga a faɗin Najeriya.
Da yake jawabi ta hanyar sanarwa a ranar Alhamis a cikin wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar Evangelist Musa D Misal da kuma Sakataren ta Sarafa Adekunle Oyewo a Bauchi, Matasan sun nuna ƙin amincewar su da Tikitin Tinubu-Shettima, suna masu shan alwashin tattara mambobin su domin zanga-zangar hakan.
Sun kuma yi kira ga Mambobin APC Kiristoci dasu jefar da Son su ga Takarar Tinubu-Shettima.
Sun bayyana mamaki na zaɓar Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Bola Ahmed Tinubu duk da kiran da ake yi ga ƴan Najeriya na dukkanin Addinai dasu kyale shi