Duk Farfesa zai riƙa ɗaukar Miliyan 2 duk wata, idan Gwamnati ta sanya hannu kan yarjejeniya — Inji Kwamiti
Duk wani Farfesa a Jami’o’in Najeriya zai riƙa ɗaukar Naira miliyan 2 a duk wata a matsayin Albashi, idan Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu tare da amincewa da shawarwari na Kwamitin ta akan yarjejeniyar Shekarar 2009 da Kungiyoyin Jami’o’i.
Kwamitin ya kuma bada shawara kan bada Alawus-Alawus duk Shekara ga Farfeso shi. Alawus-Alawus ɗin sun ƙunshi na duba manyan Ɗalibai, tafiye-tafiye, da kuɗin hatsari, da duba Jarabawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC Ta Yi Barazanar Hukunta Masu Lalata Katin Zaɓe
Sauran sun ƙunshi na duba masu manyan Digiri, da duba Jarabawar masu digiri ɗaya, da sauran wasu aikace-aikace.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa na kundin bayanan sake tattaunawa akan yarjejeniyar shekarar 2009 da aka turawa Kwamitin Shugaban Ƙasa akan Albashi, da Farfesa Nimi Briggs, Shugaban Kwamitin sake Tattaunawa akan yarjejeniyar shekarar 2009.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta The Nation taga wannan takardu na yarjejeniyar a Abuja a jiya.
Briggs yace “dukkanin takardu an miƙa su ga Ministan Ilmi Adamu Adamu