Shugaban zauren majalisar dinkin duniya, Farfesa Tijjani Muhammad-Bande, ya bayyana cewa ya zama dole mata su zama ginshikin ci gaban Nijeriya Nijeriya domin ganin an cimma manufar tsare-tsaren kare muradun karni.
Farfesa Tijjani Muhammad-Bande ya bayyana hakan ne a Abuja a yayin da ya kawo wa Nijeriya ziyara a matsayinsa na shugaban zauren majalisar dinkin duniya.
Rahotanni sun bayyana cewa; Farfesa Muhammad-Bande ya zama shugaban zauren majalisar na 74 a cikin watan Satumba.
Farfesa Tijjani Muhammad-Bande ya kalubalanci matan ne a yayin da yake tattaunawa da ministar harkokin mata a Nijeriya, Pauline Tallen, da kuma Ministar jinkai Hajiya Sadiya Umar Farouq da sauran kuma kungiyoyin mata.
Ya ce idan har ana son cimma dukkanin manufofin kare muradun karni, dole ne mata su zama gaba-gaba a dukkanin abin da muke yi. Inda ya yi tir da masu take hakkin mata, inda ya bayyana fyade a matsayin kalubale da mata ke fuskanta, kuma ya ce akwai bukatar a yake wannan dabi’a.
Ya jaddada cewa majalisar ta su za ta ci gaba da goyon bayan kawo karshen dukkanin wani cin zarafi da take hakkin mata ta hanyar bunkasa ‘yancin mata.