A jiya Laraba ne 27 ga watan Nuwamba 2019, ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky da aka fi sani da ‘yan shi’a suka ci gaba da gabatar da muzaharar kira ga gwamnati da ta gaggauta sakin jagoransu, Shaikh Ibraheem Zakzaky.
Muzaharar dai an gabatar da ita ne daga kasuwar Wuse, inda ta ci karo da harin jami’an tsaro. Jami’an tsaron sun bude wuta kan masu muzaharar, inda suka harbi wata yarinya karama ‘yar makaranta wadda ta fito daga makaranta zuwa gida kamar yadda shaidun gani da ido suka shaidawa majiyarmu.
Zuwa yanzu dai babu tabbacin ko sun yi kame ko sun harbi wadansu daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky din da suka fito muzaharar.