Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a domin halartar taron kasashe masu fitar da iskar gas (GECF) wanda zai gudana a birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea.
Malam Garba Shehu, Kakakin shugaban kasar shi ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Alhamis.
A cewar sanarwar, shugaban kasar zai halarci taron na kwana guda tare da sauran shugabannin kasashe musamman masu arzikin Iskar gas a duniya.
Daga cikin kasashen da za su halarci taron sun hada da; Algeria, Egypt, Equatorial Guinea, Libya, Bolivia, Iran, Qatar, Russia, Trinidad da Tobago, United Arab Emirates, Venezuela, Kazakhstan da Norway.
Malam Shehu ya ce wadannan kasashen suna fitar da kashi 70 zuwa 80 na iskar gas da ake amfani da shi a duniya.
A cikin watan Nuwamban 2015, shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ya halarci irin wannan taron a birnin Tehran na kasar Iran. Kuma a shekarar 2011 Nijeriya ta halarci irin taron a birnin Doha na kasar Qatar.
Taron a birnin Malabo a wannan karon, shi ne irinsa na farko a kasar Afrika.
A ranar 19 ga watan Nuwamba ne, shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin Gabriel Mbega Obiang Lima, jami’in shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, wanda ya zo ya kawo wa shugaban Nijeriya takardar neman halartar taron, tare da godewa Nijeriya bisa gudummawar da ta bayar domin gudanar da taron.
A lokacin ziyarar, shugaban kasa ya ce Nijeriya tana fitar da iskar gas fiye da man fetur.
Malam Shehu ya ce daga cikin wadanda za su yiwa shugaban kasar rakiya sun hada da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; karamin ministan man fetur, Timipre Sylva; ministan ma’adinai da karafa, Olamilekan Adegbite; sai kuma Daraktan Kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari.
Garba Shehu ya ce bayan kammala taron, shugaba Buhari zai wuce garin Daura dake jihar Katsina domin kwashe kwanaki biyar a wata ziyarar da zai kai.