Tun bayan umarnin babban sifeton yan sandan kasa kan hana amfani da kakinsu ba bisa ka’ida ga masu fina finan Hausa, yanzu haka lamarin na ci gaba da fuskar hankali.
Wasu daga cikin masu harkar fim din Hausa na Kannywood wadanda wannan umarni na ‘yan-sanda ya shafi aikinsu a nasu bangaren na ci gaba da mayar da martani.
Aminu Saira, fitaccen mai bayar da umarni ne a fina-finan Kannywood, kuma ya shaida wa BBC cewa za su duba su gani idan umarnin na Babban Sufeton ‘yan-sandan Najeriyar yana kan doka za su kiyaye.
Idan kuma suka duba suka ga su ma abin da suke yi yana kan doka to za su hada kai da abokan aikinsu na Kudancin Najeriya su kalubalanci umarnin a kotu, in ji shi.
“Domin da mu da su duk doka ce ta kirkire mu a Najeriya.”
Ya kara da cewa, “Duk wanda yake zaune a kasarnan da jami’in gwamnati da wanda ake mulka da mai mulki da ko waye suna karkashin doka ne.’’
“Saboda haka idan doka ta kasa ta haramta mana mu nuna kayan ‘yan-sanda kuma mu yi amfani da su a cikin fim dole za mu girmama dokar kasa kuma mu hakura ba yadda za mu yi,’’ in ji daraktan.
Ya kara da cewa: “Amma in doka ta ba mu dama to za mu yi yaki batun iya iyawarmu, iya karfinmu da mu da na Kudu da na Arewa mu hadu in ya so ita dokar kasa ta fito ta fassara cewa haramun ne mu yi amfani da shi ko kuma a’a ba haramun ba ne kuna da dama ku yi amfani da shi.’’
DUBA WANNAN LABARIN; Inter Milan zata warware kwantiragin Alexis Sanchez
Ya ce za su yi hakan ne domin kotu ta fayyace abin da doka ta ce a game da abubuwan da suke yi a fim kan ‘yan-sandan.
Daraktan ya kara da cewa su daman duk abin da suke yi a kan doka suke yinsa sai sun samu izini.
Ya ce akwai matsaloli da abubuwa da suka faru a baya wanda har Kwamishinan ‘yan-sanda ya fito aka yi maganganu a baya, wanda a lokacin aka ce duk wanda zai yi abin da ya shafi ‘yan-sanda sai ya samu izini.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Umarnin da Babban Sufeton ‘yan-sandan Najeriya ya bayar ga masu shirya fina-finai su daina amfani da kayan sarki na ‘yan-sanda da kuma daina muzanta aikin dan-sanda a shirye-shiyensu na talabijin, ko zane ba tare da izinin rundunar ba, ya ja hankalin masu sana’ar.
A umarnin Usman Baba ya ce daga yanzu rundunar ba za ta amince da yadda ake amfani da kayan-sarki da sauran abubuwa na ‘yan-sanda ba a fina-finai, ba tare da izini ba kamar yadda doka ta tanadar.
Ya ce idan ba haka ba to kuwa duk wanda ya karya doka zai ɗanɗana kudarsa.
Sanarwa da kakakin rundunar na kasa CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce “ka da wani mai shirya fina-finai da ya sake nuna ‘yan-sanda a matsayin marasa kirki ba tare da izini ba a rubuce daga rundunar yan-sanda.”
Sanarwar ta ƙara da cewa ba za ta amince da bayyana aikin ɗan-sanda ba a fina-finai, matsawar abin da aka kwaikwaya a aikin ba shi da kyakkyawan tasiri ga al’umma.