Kungiyar Inter Milan ta cimma yarjejeniya da Alexis Sanchez domin katse kwantiraginsa.
Yanzu dan kasar Chile din zai bar kulob din nan take, inda ya zai zama dan wasa da zai iya tafiya wata kungiyar Kyauta a wannan bazarar.
Wani masani kan harkokin wasanni Fabrizio Romano ya tabbatar da hakan a ranar Litinin.
Romano ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, “Inter ta cimma yarjejeniya bisa ka’ida tare da Alexis Sanchez don kawo karshen kwantiraginsa a halin yanzu, inda yanzu ake jiran kammala wasu sharidodin karshe kafin sanya hannu kan wannan sabuwar yarjejeniya.
KARANTA WANNAN LABARKN: Sanatan APC Ya Hassala Kan Matsalar Tsaro, Ya Buƙaci Babagana Monguno Ya Sauka
“Sanchez, na daya daga cikin yan wasan da ake sa ranan Olympique Marseille zata dauka kyauata a wannan kakar yayin da wasu kungiyoyin ke cigaba da njna sha’awar daukar shi.”
Sanchez ya koma Inter ne daga Manchester United kyauta a shekarar 2020.
Dan wasan mai shekaru 33 ya zura kwallaye 20 kacal kuma ya taimaka aka zura kwallaye 23 a wasanni 108 da yafafattawa Inter Milan.
A wani labarin kjma na daban.
Sanatan jam’iyyar APC ya bayyana bacin ransa kan matsalar tsaro, ya bukaci Babagana Monguno ya yi murabus
A jiya Lahadi, Wani dan majalisar dattawa na jam’iyyar APC mai mulki, Sani Musa, ya yi kira ga mai bawa Shugaban Kasa shawara akan harkokin tsaro Babagana Monguno da ya yi murabus a matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA).
Sanata Musa wanda ya fito daga Nijar – daya daga cikin jihohin da hare-haren ‘yan ta’adda suka fi ta azzara ya yi tir da tabarbarewar yanayin tsaro a fadin kasar nana.
Ya yi imanin Monguno, Manjo Janar mai ritaya kuma tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasa, ba shi da wani dalilin da zai sa ya ci gaba da zama a matsayin babban mai tsare-tsare kan harkokin tsaron Najeriya yayin da ake ci gaba da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Kafar yada labarai ta Channels TV ta ruwaito cewa, masu dauke da makamai wadanda ba jami’an gwamnati ba ne, da suka hada da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, sun kara kaimi a baya-bayan nan, inda suka kara kai hare-hare kan jami’an tsaro kamar gidan gyaran hali da ke Abuja da wasu jami’an tsaro a sassan kasar nan
Daya daga cikin irin wannan harin shi ne harin da aka kai wa dakarun rundunar tsaron fadar shugaban kasa da ke bada tsaro ga fadar gwamnatin tarayya da kuma babban birnin Tarayya Abuja, inda aka ce an kashe wasu sojoji a gayin harin..