Buhari yayi jawabi bayan Dangote, Hadiman sa, sun samu Lambar yabo mafi girma a Jamhuriyar Nijar
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya taya wasu mukarrabansa biyu: Sarki Abba, Babban mataimaki na musamman kan harkokin gida da Ambasada Lawal Kazaure, Babban jami’in tsare-tsare, bisa karramawar babbar lambar yabo ta farar hula na jamhuriyar Nijar.
Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya fitar da sakon taya murna na Shugaba Buhari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ko kaɗan ba mu damu ba – PDP ta caccaki APC kan ƙalubalantar zaɓen Gwamnan Osun
Shugaban wanda ya karbi waɗanda suka samu Lambobin yabon da aka ba su, ya ce ya dauki wannan karramawar da aka yi musu a matsayin wata alama ta dadadden zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu da al’ummarsu.
Ya kuma bayyana fatansa cewa, dadadden zumunci da haɗin gwiwar da ke tsakanin ƙasashen biyu za su ci gaba da bunƙasa.
Shugaba Buhari ya kuma miƙa gaisuwar ban girma ga Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa da Mohammed Matawalle na jihar Zamfara, da ‘yan kasuwa, Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote da Abdulsamad Rabi’u, shugaban kungiyar BUA, wadanda suma aka karrama su da lambar yabo ta kasar Nijar a wajen taron Bikin Ranar Ƴancin Kai.
Shugaban ya godewa Shugaba Mohammed Bazoun da ƴan Nijar bisa wannan karramawar da aka yi musu.