Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumomi a jihar Filato dake arewa ta tsakiya a Najeriya sun kwace lasisin duk wasu makarantun yara masu zaman kansu daga Nursery,firamare, kananan sakandire da manyan sakandire da ke aiki a fadin jihar.
Gwamnatin jihar ta bakin kwamishiniyar ilimi Elizabeth Wapmuk, yayin da take zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a Jos, ta ce matakin ya zama dole saboda karancin aiki, rashin bin ka’idojin gwamnati da sauran batutuwan da makarantu masu zaman kansu ke yi.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Dole ne a daina kashe Ƴan Arewa a Kudu maso Gabas – Dattawan Arewa
A cewar Kwamishiniyar Ilimin, ayyukan rashin da’a da wasu makarantun ke yi na yin illa ga ilimi a fadin jihar.
Ta kara da cewa, “Rahotanni masu inganci sun nuna cewa wasu daga cikin Makarantun masu zaman kansu sun boye harabar su domin kaucewa binciken wuraren da ke zama maboyar miyagun ayyuka da kuma yawaitar Makarantu masu zaman kansu da ba su yi rajista ba a cikin Jihar sun yi wa Jihar illar da ka iya haifarwa ilimi”.
Wapmuk, ta ci gaba da bayanin cewa duk wadanda ke da niyyar gudanar da Makarantu masu zaman kansu a jihar za su zo ne domin neman amincewa da kuma sabunta takardar shaidarsu domin ma’aikatar za ta fara aikin tantance korafe-korafen masu mallakar makarantun.
Majiyar JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa akwai makarantu masu zaman kansu sama da dubu biyar da ke aiki ba tare da lasisi ba a jihar Filato.
“Kashi 85% na 485 makarantu masu zaman kansu da aka baiwa lasisi sun sabawa ka’idojin su. Kashi 90% na makarantu masu zaman kansu ba sa bin manufofin Gwamnati da umarnin ta.”
A Wani Labarin Kuma Mai Magana da Yawun Ƙungiyar Dattawan Arewa NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya fitar da gargaɗi kan kashe ƴan Arewa a yankin Kudu maso Gabas.
Baba-Ahmed ya ce kai hari da kashe ƴan Arewa a yankin Kudu maso Gabas yana da haɗari.
Ya yi nuni da cewa irin wannan mataki na iya dagula dangantakar al’umma a wasu sassan Najeriya.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, kakakin NEF ya ce ya kamata ƴan siyasa masu neman kuri’a su fito fili su yi Allah-wadai da irin waɗannan ayyuka.
Ya kuma jaddada cewa dole ne a daina irin wannan ga ƴan Arewa.
Baba-Ahmed ya rubuta: “Ya kamata a yi Allah-wadai da hari da kashe-kashen da ake yi wa ’yan Arewa, musamman a Kudu maso Gabas, kuma a daina.
“Yana da matukar hadari domin zai iya kawo tabarbarewar dangantakar al’umma a wasu sassan Ƙasar nan.
“Muna bukatar mu ji karara da kuma yin Allah wadai daga masu son kuri’un mu