Hare-haren da Isra’ila ta kai a ranar Juma’a ta kashe akalla mutane 10 ciki har da wani kwamandan kungiyar yan Jihad, yayin da fargabar barkewar yakin Gaza ya sake mamaye yankin Falasdinawa da aka yi wa kawanya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Ana iya jin karar fashewar abubuwa da dama a duk fadin Gaza.
Ana iya jin gunjin jiragen leken asirin Isra’ila suna shawagi a sararin samaniyar.
Hare-haren sun biyo bayan zaman dar dar da kungiyar Jihad ta Islama suka yi na kwanaki bayan kama babban shugaban Falasdinawa Bassam al-Saadi a birnin Jenin da ke yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye.
Ghazi Hamad, wani babban jami’i na Hamas – kungiyar da ke mulki ya ce harin na baya-bayan nan “laifi ne, kisan kiyashi da Isra’ila ta yi wa mutanenmu”.
Hamad ya shaida wa Al Jazeera cewa babu “ba wata hujja” game da hare-haren, yana mai cewa bangarorin Falasdinawa na da ‘yancin kare kansu da kuma “kare” mutanensu.
Ana iya ganin an harba makaman roka da yammacin Juma’a daga Gaza zuwa Isra’ila a martanin farko na Falasdinawa.