Daga: Abbas Yakubu Yaura
A sakamakon ganawar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas suka yi, an kafa wani kwamitin mutane 14 da za su tuntubi tare da bayar da shawarwarin ga dukkanin mutanen biyu za su yi la’akari da su.
Wata majiya mai karfi ta jam’iyyar da ke da masaniya kan ci gaban ta bayyana wa Jaridar Sunday Vanguard cewa har yanzu ba a bayyana mambobin kwamitin ba saboda har yanzu ba a sanar da wasu daga cikinsu a hukumance ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Dan Takarar Gwamnan Zamfara Na PDP Ya Karyata Jita-jitar Sauya Sheka Zuwa APC
Majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai, ta bayyana cewa ana sa ran kwamitin zai fara aiki da gaggawa.
Jam’iyyar PDP ta fada cikin rikici tun bayan da Atiku ya zabi Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.
Wannan ci gaban ya sabawa tunanin da wasu ke yi na cewa Wike ne zabin dabi’a bayan ya zo na biyu a zaben fidda gwani wanda ya samar da Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa makwanni biyu kacal da suka gabata Atiku da Wike sun yi musayar zafafan kalamai kan batun abokin takara.
Hakan ya kai ga taron kwamitin amintattu na PDP wanda ya yi yunkurin sasantawa.
Majiyar ta ce “Mun samu ci gaba mai kyau a cikin sa’o’i 24 da suka gabata bayan ganawar da dan takarar mu na shugaban kasa, Atiku Abubakar, da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike suka yi.”
“Taron da ya baiwa makiya jam’iyyar mu mamaki, ya kawo rudani tare da maido da fata wajen ganin an gaggauta warware abin da ‘yan adawar mu ke dauka a matsayin babban rikici. ”
Da aka tambayi majiyar ko wane irin sharudda da aka bayar da kuma irin rangwame aka yi, majiyar ta ce, “Batun sharudda bai taso ba a lokacin da dukkan mutanen biyu suka ajiye sabanin da ke tsakaninsu, suka yi magana da juna.”
“Tabbas mabiyansu za su yi la’akari da wannan kuma su fada cikin layi. Abin da ke ƙasa yanzu yana neman hanyar ci gaba.”
“Shawarwarin da kwamitin mai wakilai 14 ya bayar, za a yi la’akari da su tare da daukar mataki. Ina mai tabbatar muku da cewa kwamitin yakin neman zaben zai bi bayansa.”
Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan rikicin da ke faruwa a jam’iyyar, sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba za a warware duk wasu batutuwan da suka kunno kai a Jam’iyyar.
Ya ce, “PDP iyali ne mai girma kuma kamar yawancin iyalan mutane akwai batutuwa amma ina farin cikin sanar da ku cewa muna da gabobi, matakai da hanyoyin magance matsalolinmu.
“Ba mu zama kamar jam’iyyar APC da ke nutsewa ba, ban tuna wani taro da kwamitin amintattun su suka yi ba, BoT dinmu ya gana kuma sun kafa kwamiti don sasanta tsakanin dan takararmu da Gwamna Wike.”