Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya amince da fitar da Naira miliyan 19.3 domin biyan alawus-alawus na tallafin karatu ga dalibai 59 da suka samu shiga makarantun lauya cikin gaggawa.
Sakataren zartarwa na hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Borno, Mallam Bala Isa ya bayyana haka ranar Talatar nan a Maiduguri yayin da yake zantawa da manema labarai.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Bala ya ce tallafin na shekarar karatu ta 2021/2022 ne.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/gwamnatin-jihar-gombe-ta-kaddamar-da-rundunar-ofureshin-hattara/
“Wannan wani bangare ne na jajircewar mai girma gwamna wajen taimakawa bangaren ilimi da kuma taimakawa daliban jihar Borno a kowane mataki na ilimi.
“Muna godiya ga mai girma gwamna da wannan tallafi kuma mun yi imanin cewa daliban za su yi iya kokarinsu don ganin sun sanya Borno alfahari,” in ji Isa.
(NAN)