Ruguza tsarin ilmi ne biyan ASUU Albashi – Jigon APC, Lukman
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Salihu Lukman ya ce har sai gwamnatin tarayya ta bullo da tsarin rashin aiki, babu albashi, mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) za su ci gaba da rike kasar nan, don yin fansa saboda yajin aikin da suke yi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mamboin Mu A Edo Da Suka Koma Jam’iyar PDP Sun Yaudaremu—Jam’iyar APC
Lukman ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja yayin wata tattaunawa da Manema Labarai da wasu zababbun ‘yan jarida, inda ya jaddada cewa, al’ada ce mai barna a biya ma’aikatan dake yajin aiki albashi.
Ya na mai ra’ayin cewa zuba jari a fannin ilimin jama’a abu ne da bai kamata a yi wasa da shi ba.
Jigon jam’iyyar ya lura cewa ya kamata Najeriya ta koma kan tsohon tsarin da manufofin IMF/Bankin Duniya suka ruguza, yana mai jaddada cewa babu wata kasa da za ta ci gaba ta hanyar samar da kudade masu zaman kansu na bangaren ilimi.
Lukman ya ce, “Tun a shekarar 1985 rikicin da muke fama da shi shi ne, an daskare zuba jari a fannin ilmin jama’a wanda ya haifar da gibin da muke da shi a yau, inda muke da ‘ya’ya amma babu makarantun da za su je; inda muke da makarantu amma babu malamai; inda muke da makarantu, babu kayan koyarwa”.
Ya jaddada cewa wani bangare na rikicin da ya zama dole a warware shi ta hanyar siyasa shi ne dawo da hayyacinsa a bangaren da ke da matukar muhimmanci.
Jigon jam’iyyar ya dage cewa tsara yadda ASUU ke tafiyar da harkokinta da kuma tabbatar da cewa ta yi daidai da mafi karancin ma’auni da zai tabbatar da ci gaban matasa ya zama dole.
Lukman ya kara da cewa: “Yanzu, abin takaici, hatta wadanda ake kira da ‘yan boko, ban ga wani hankali a tattaunawar da ASUU ke jagoranta ba.
“Je ka karanta labarin da na rubuta na karshe game da yajin aikin ASUU a lokacin da suka samu yarjejeniyar kusan Naira biliyan 30 daga gwamnatin tarayya. Na yi tambaya: bayan an kashe Naira biliyan 30, daga ina za a yi zagaye na gaba? Domin za a sake samu kuma wannan shine tarkon da muke ciki.
“Kuma abin takaici ma mun samar da al’adar da ba ta dace ba, ko ASUU ta yi aiki ko ba ta yi ba, muddin suna yajin aiki, duk lokacin da suka koma sai a biya su. Dangane da abin da ya shafi ‘yan kungiyar ASUU, a wannan lokaci da suke yajin aikin gwamnati na taimaka musu wajen ceto. A halin yanzu, yaranmu suna zaune tare da mu a gida.